Fitattun 'yan wasan Ukraine da suka dauki makamai
'Yan wasan Ukraine da dama da suka yi fice a wasannin dabam-dabam, sun yanke shawarar daukar makamai domin su kare kasarsu daga mamayar Rasha. Ga kadan daga cikinsu.
Dmytro Pidruchnyi dan wasan (Zamiyar Kankara)
Bayan ya koma gida daga gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 wato Olympic da aka gudanar a Beijing, Dmytro Pidruchnyi ya gabatar da kansa ga rundunar sojojin Ukraine sakamakon mamayar da Rasha ke wa kasarsa. Mai shekaru 30 a duniya, tsohon zakaran wasan zamiyar kankara a nahiyar Turai ya kuma halarci wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympic har sau biyu.
Vitali Klitschko dan wasan (Dambe)
Guda daga fitattun 'yan wasan Ukraine, Vitali Klitschko ya lashe gasar dambe ajin masu nauyi a shekarun 2000. Ya kuma kare kambunsa har sau 12. Shi ne magajin birnin Kyiv fadar gwamnatin Ukriane tun daga shekara ta 2014. Mai shekaru 50 a duniya, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa a shirye yake ya dauki makamai, domin ya kare kasarsa.
Vladimir Klitschko dan wasan (Dambe)
Vitali ya kaksance wa ga Vladimir Klitschko zakaran dambe a wasan guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympic a shekara ta 1996. Ya kuma zama zakara a mayan wasannin dambe dabam-dabam na duniya. Ya yi murabus daga wasan dambe a shekara ta 2016, amma mai shekaru 45 a duniyar, ya shiga cikin rundunar sojin Ukraine domin taimakon kasarsa a yakin da take yi da Rasha kamar yadda yayansa ya yi.
Sergej Stachowski dan wasan (Tennis)
Tsohon dan wasan Tennis Sergej Stachowski ya yi fice ne bayan da ya lallasa takwaransa Roger Federer a zagaye na biyu na gasar Wimbledon a shekara ta 2013, lokacin da aka sanya shi a matsayi na 116 a jerin 'yan wasan Tennis mafiya kwarewa a duniya. A yanzu mai shekaru 36 a duniyar, ya koma Ukraine domin shiga yaki da matakin Rasha na mamaye kasar a karshen watan Fabarairun 2022.
Oleksandr Usyk dan wasan (Dambe)
Usyk fitaccen dan wasan dambe, ya taba lashe gasar dambe ajin masu nauyi ta duniya. Zakaran wasannin dambe dabam-dabam. Mai shekaru 35 a duniya, ya lashe wasan dambe a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta shekarar 2012. Ya shiga rundunar sojojin Ukraine, domin kare kasarsa. Usyk ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, ba ya son ya yi harbi ko kisa amma ba shi da zabi.
Oleh Luzhnyi dan wasan (Kwallon Kafa)
Tsohon mai tsaron baya Oleh Luzhnyi ya lashe gasar Premier League da kofin kalubale a Ingila, yayin da yake bugawa kungiyar Arsenal wasa a farkon shekarun 2000. Mai shekaru 53 a duniya, ya koma gida domin shiga yakin da kasarsa ke yi da Rasha. Ya bayyana cewa yanayi ne na tashin hankali. Ya ce yana son zuwa Ingila ya horas da 'yan wasa, amma kasarsa da al'ummarsa sune kan gaba.
Vasiliy Lomachenko (Zakaran Damben Duniya)
Guda daga cikin fitattun 'yan dambe daga Ukraine, sau biyu Lomachenko na lashe gasar dambe ta wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympic kafin ya lashe gasar dambe ta duniya har sau uku. Ya lashe kyauta a watan Disambar 2021, bayan samun nasara kan Richard Commey. Mai shekaru 34 a duniyar ya shiga rundunar sojojin Ukraine a garinsa na haihuwa Bilhorod-Dnistrovskyi, domin yakar Rasha.
Yuriy Vernydub (Mai Horas da 'Yan Wasan Kwallon Kafa)
Vernydub shi ne mai horas da 'yan wasan kungiyar Sheriff Tiraspol. Kungiyar ta Moldova ta lallasa Real Madrid da ci biyu da daya, yayin gasar cin kofin zakarun Turai a watan Satumbar 2021. Mai shekaru 56 a duniya, tsohon dan wasan bayan ya shiga rundunar sojojin Ukraine domin yakar Rasha. Ya bugawa kungiyar Zenit Saint Petersburg ta Rasha, a gasar lig din kasar daga shekara ta 1997 zuwa 2000.
Yaroslav Amosov dan wasan (Kokawa)
Shahararren dan wasan kokawa Amosov ya kasance zakaran kokawa na duniya. Mai shekaru 28 a duniya, ya kudiri aniyar kare Ukraine. Hakan na nufin ya sarayar da damar kare kambunsa, a fafatawar da zai yi da Michael Page cikin watan Mayun wannan shekara ta 2022.