1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fito-na-fito tsakanin 'yan sandan Girka

September 6, 2012

Taƙaddama ta ɓarke a tsakanin 'yan sandan Girka bisa boren adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.

https://p.dw.com/p/164Th
Riot police stand next to a burning election kiosk of an independent right-wing candidate by protesters during a May Day protest in Athens, Tuesday, May 1, 2012. In debt-crippled Greece, more than 2,000 people marched through central Athens in subdued May Day protests centered on the country's harsh austerity program. The Greek elections are scheduled for Sunday, May 6. (Foto:Thanassis Stavrakis/AP/dapd).
Hoto: dapd

A wannan alhamis ne wasu 'yan sandan ƙasar Girka da ke boren nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati suka kafa shinge a hedikwatar 'yan sandan kwantar da tarzoma na ƙasar, inda suka hana wasu motocin safa-safa da ke ɗauke da 'yan sandan kwantar da tarzomar ficewa daga farfajiyar hedikwatar domin zuwa babban filin da 'yan sandan da ke boren ke shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a ƙarshen mako.

Taƙaddama dai ta ɓarke a lokacin da wasu 'yan sandan kwantar da tarzomar suka yi ƙoƙarin fatattakar takwarorin aikin su, waɗanda galibin su ke sanye da kaki, kana suke ta furta kalaman yin Allah wadai da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati ɗauke da allunan da ke yiwa hukumomin tofin Allah tsine.

Ɗaya daga cikin jami'an 'yan sandan da ke boren ya ce ba za su taɓa kyale motocin Bus-Bus na 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa garin Thessaloniki ba, wanda zai karɓi baƙuncin kasuwar baje kolin da a lokacin ta ne kuma masu bore suka shirya gudanar da wata zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun da gwamnatin Girka ke aiwatarwa.

Kazalika in anjima kaɗan ne wasu 'yan sanda da jami'an kwana-kwana ma za su gudanar da wata zanga-zangar adawa da shirin tsuke bakin aljihun a tsakiyar Athens, babban birnin ƙasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas