1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan na tunawa da iftala'in girgizar kasa

Abdourahamane Hassane
March 11, 2023

Japan na tunawa da cika shekaru goma sha biyu da aukuwar iftala'in girgizar kasa mafi muni da aka taba samu a duniya.

https://p.dw.com/p/4OY5s
Japan beginnt noch in diesem Jahr mit der Freigabe von aufbereitetem Wasser aus Fukushima
Hoto: Charlie Triballeau/AFP

Girgizar ta haddasa mummunar igiyar ruwa ta Tsunami,da ta janyo bala'in tashar nukiliyar ta Fukushima.da ke a Daiichi. Kamar kowace shekara, an yi shiru na minti daya a kasar da misalin karfe biyu na rana, karfe biyar agogon GMT. Girgizar kasar mai karfin maki tara a maunin Richter da ta afku a dukkannin tsibiran kasar na Japan  har zuwa China a lokacin da ta afku a ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2011, ta kashe rayukan mutane sama da dubu 18 yayin da wasu dubbai suka yi batan dabo.