Fursunoni sama da 17,000 sun rasu a Siriya
August 18, 2016Fiye da Fursunoni yaki 17,000 ne suka rasu sakamakon cin zarafi da wasu nau'oi na cututtuka da suka kamasu, a lokacin da gwamnatin Siriya ke tsare da su a tsawon shekaru biyar a cewar Kungiyar Amnesty International.
Kungiyar ta ce wadannan Fursunoni sun rasu sakamakon gallazawa da cin zarafi da suka hadar da aikata lalata da dauresu, wasunsu da daura musu tayar mota hadi da shan duka ko zare musu farata da sauran nau'oi na azabtarwa. Wannan dai ya sanya mutane da dama sun rasu a cewar rahoton kungiyar, da ya fita bayan tattaunawa da wasu kimanin mutane 65 da suka rayu bayan shan azaba a hannun mahukuntan na birnin Damaskus.
Philip Luther shi ne daraktan kungiyar ta Amnesty International mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka ya yi karin haske;
"Abin da ke faruwa a bayan idanun jama'a take hakki ne na bil Adama a Siriya, akwai cutarwa da ta sabawa tunani da mahukunta Siriya, ke wa wadanda suka tsare tun daga shekarar 2011".