Fushin Amirka da masu hulɗa da Snowden
June 24, 2013Kakakin Fadar White House na Amirka Jay Carney ya ce ƙasashen da Edward Snowden, ma'aikacin kwantiragin da ya falasa bayyanan sirrin da Amirka ke tatsa, ke neman mafaka sun kawar da duk wani iƙirari da yake yi na cewa burinsa na ganin a yi abubuwa a bayyane ne, ta yadda za'a kare 'yancin faɗan albarkacin baki da kuma sauran haƙƙoƙin ɗan adam.
Lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai Carny ya ce idan dai har burinsa shine ganin an kare 'yancin 'yan jarida, a kuma tabbatar da cewa mutane sun yi amfani da kafar sadarwa ta internet cikin walwala, to ko bai zaɓi abokan hulɗar ƙwarai ba.
A waje guda kuma wasu rahotannin sun ce Julian Assange wanda shi ma ake zargi da kwarmato bayanan sirrin Amirkan na taimakwa Edward Snowden.
Duk da cewa ana samun bayyanai masu karo da juna kan inda Snowden ya ke, Assange ya ce yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana magana da lauyoyinsa daga duk inda ya ke, hasali ma shi ne ya ke neman ma sa mafaka a ƙasar Ecaudor, wadda a ofishin jakadancinta na Landan ya tare na tsawon shekara guda yanzu.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman