1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20: Haduwar farko tsakanin Trump da Putin

Salissou Boukari
July 7, 2017

A wannan Juma'ar ce ake haduwar farko ta keke da keke tsakanin shugaba Donald Trump na Amirka da shugaba Vladimir Putin na Rasha a daura da babban taron kasashe 20 masu karfin masana'antu.

https://p.dw.com/p/2g75c
Kombobild Trump Putin
Shugaban Amirka Donald Trump da na Rasha Vladimir Putine

A jajibirin wannan haduwa shugaban na Amirka ya furta kalammai tun daga birnin Varsovie inda ya zargi Rasha da nuna halaye na raba kanu, da kuma yin shishigi a zaben shugaban kasar Amirka da ya gudana na 2016.

Sai dai irin zafin da ake sa ran wannan tattaunawa za ta yi tuni ake ganinsa a wajen zauran taron, inda dubban masu zanga-zanga daga sassa daban-daban na duniya suka hallara a birnin na Hamburg domin nuna adawarsu ga taron na G20.

Wata arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro ta yi sanadiyyar jikkatar 'yan sanda 76.

Shugaban kasar ta Amirka bayan ya nuna yabo ga shugaban Rasha a baya, ya ja da baya kan irin huldar da ya son kullawa da kasar ta Rasha sakamakon tarin zargin da aka yi masa na huldar boye da kasar ta Rasha.