G20 za ta dauki mataki kan kin biyan haraji
September 5, 2016Kungiyar G20 za ta dauki wasu sabbin matakai na yaki da haramtacciyar tabi'ar boye kudade da wasu kamfanoni ko wasu attajirai ke yi a wasu bankunan bayan fage da nufin kauce wa biyan haraji a cikin kasashensu.
A wata hira da ya yi da kafofin yada labarai na kasar Faransa ministan kudi da tattalin arziki na Faransa Michel Sapin ya sanar da hakan inda ya ce sanarwar karshen zaman taron kungiyar ta G20 da za a fitar a wannan Litinin za ta kunshi bukatar ganin an fitar da wani bakin kundi da zai kunshi jerin sunayen haramtattun wuraren bayan fage da ake boye kudaden da nufin kin biyan harajin, tare kuma da daukar matakan yin hukunci mai tsanani a kai.
Wannan dai shi ne karo na farko da wata sanarwar karshen zaman taron kungiyar ta G20 za ta kunshi matakai na zahiri kan wannan matsala ta boye kudade da ake yi da nufin kin biyan haraji, lamarin da ministan ya ce na taimakawa ga tauye tattalin arzikin duniya baki daya.