Kasashen G7 na daukar China a matsayin barazana
May 4, 2021Talla
A wata hira da manema labarai a gabanin taron kolin kungiyar, babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, ya bayyana cewa manufar da kasashen suke son cimma ita ce na tilasta wa sauran kasashe amfani da sharudan da duniya ta cimma, ciki har da kasar China da ke barazana ga batun kare 'yancin bani Adama ga masu rajin girka dimukuradiyya a Hong Kong, hakan da ma tsirarrun Musulmai 'yan kabilar ouïghoure Xinjiang.
Rahotanni sun ce ko baya ga taron na ministocin harkokin wajen, a nasu bangare suma ministocin kudi menbobin kungiyar ta G7 za su gabatar da nasu taron daga yau zuwa gobe a birnin Landan.