Taron G7 ya jaddada goyon baya ga Ukraine
June 27, 2022A cigaba da taron kolin da suke gudanarwa a kudancin Jamus, Shugabannin kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na duniya sun jaddada anniyarsu ta ci gaba da taimakon Ukraine da ke fuskantar mamaya daga Rasha, tare da kira ga Rasha da ta kawo karshen yakin da ke yi a Ukraine.
Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya yi jawabi ta bidiyo ga mahalarta taron, inda ya bukaci a cikin gaggawa kasashen masu karfin tattalin arzikin masana'antu, su agazawa kasar domin ganin an kawo karshen zubar da jini kan nan zuwa karshen wannan shekara.
Kasashen G7, sun bayyana matsaya guda ta karin matsin lamba ga Rasha, har sai ta dakatar da mamayar da ta ke wa Ukraine, da ma saka mata wasu karin takunkumi.
Batun sauyin yanayi da yunwa da talauci na cikin batutuwan da shugabannin ke tattaunawa a yayin taron. Shugaban Afirka ta Kudu da takwaransa na Senegal Macky Sall da ke shugabancin Kungiyar Tarayyar Afirka na daga cikin wadanda ke halartar taron, kana batun hanyoyin samar da makamshi na daga cikin wasu muhimman batutuwan da shugaban zai tattauna akai da kasash masu karfin tattalin arziki na duniya.