Taron G7 ya cimma warware matsaloli
June 9, 2015A sanarwar karshen taron da suka kammala a wannan Litinin a Chloss Elmau da ke kudancin Jamus, shugabannin kasashen guda bakwai masu karfin tattalin arzikin masana'antu a duniya G7, sun cimma manufofin a kan al'amuran tattalin arziki wanda ake ganin zai yi tasiri a duniya da maganar yaki da taadancin da rikicin ukraine da kuma dumamar yanayi.
Kasashe guda bakwai mafi karfin tattalin arziki a duniya, su dukkaninsu sun yi amanar cewar matsalar dumamar yanayi wani babban kaubale daka iya zama sanadin koma baya ga ci gaban tattalin a arzki a duniya idan har ba a rage kaso a yawan hayakin iskan gas da kamfanoni da masantu sukan fitarwa ba. Tun a shekarun 2009 a taron Copenhagen kan yanayi.
Batu da shugabannin kasashen duniyar suka gaza cimma matsaya daya suke ta fafutukar ganin an daidaita. Kuma yanzu kasashen na G7 zasu je a murya daya a taron Paris kan yanayin da a yi a cikin watan Disamba domin ganin an cimma wata yarjejeniya bayan da aka kwashe shekaru da dama ana yin kai da komo a kan batu.b
Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus mai masaukin baki na taron ta yi tsokaci kamar haka:
''Mun sani muna bukatar rage mafi zurfi na hayakin gas din da ake fitarwa a duniya wanda kuma wani sai kasance wani babban hobasa na daidaita al'amuran tattalin arziki na duniya a duk tsawon karnin da muke cikinsa.''
A kudirin da aka cimma a shekarun 2010 kasashen sun gabatar da shawarar cewar, kafin nan da shekarun 2050 an rage yawan hayakin iska mai guba da kamfanonin da masana'antu na duniya sukan fitar da kishi 40 zuwa 70 cikin 100.
Kasahen dai na son shinfida wani tsarin bai daya na samar da hanyoyin samar da wasu kudaden na kafa wata gidauniya domin yin rika kafi ko tinkarar wasu mayan matsaloli na rayuwar da gobe da kasahen ka iya fuskanta. Sai dai wasu kungiyiyoyin masu zaman kansu na yin suka a kan shirin