SiyasaTurai
Ukraine: G7 ta yi fatali da bukatar Rasha
March 28, 2022Talla
Gaggan kasashe masu karfin tattalin arzikin nan guda bakwai na G7 sun yi watsi da bukatar Rasha ta daga yanzu su rika sayen makamashin iskar gas da takardar kudin Rasha ta ''ruble''. Ministan kula da makamashi na Jamus Robert Habeck ne ya shaida wa 'yan jarida haka a wannan Litinin.
Masana tattalin arziki sun ce dabara ce da Shugaba Putin ke da ita a yunkurinsa na ganin ya tayar da komadar darajar takardar kudin Rasha ta ''ruble'' wace ta fadi tun bayan mamayar da ya yi wa kasar Ukraine.
Kasar Rasha ce dai ke zama babbar mai samar da makamashin iskar gas ga galibin manyan kasashen duniya masu arziki na G7, inda suke amfani da gas din wurin dumama dakuna a lokacin hunturu da kuma samar wa da kansu lantarki.