Sake fasalta harajin duniya daga G7
June 4, 2021Taron birnin Landan zai tattauna ne kan batun sake fasalta harajin duniya, tare da duba yiwuwar cimma matsaya kan kudaden harajin da kamfanoni musamman ma da ke amfani da fasahohin zamani ke bayyanawa, inda ministan kudin Birtaniya Rishi Sunak, ya ce yana da kyau a yi wa batun kallo da idon basira yana cewa "Ina da yakinin cewa wannan taro zai kasance mana wata dama ta tinkarar muhimman kalubalai a cikin gagawa da ke addabar tattalin arzikin duniya." Ko baya ga batun harajin duniya taron zai kuma duba batun raba daidai na allurar rigakafi a kasashen duniya, kana kuma taron dai na a matsayin wani na share fage ne kan wani taron kolin kasashen da za su gabatar a ranar 11 ga wannan watan wanda ake hasashen shugaban Amirka Joe Biden zai halarta.