G7: Ukraine da Japan sun kulla hadin gwiwar tsaro
June 13, 2024Talla
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya, Shugaba Volodmyr Zelensky ya ce Japan za ta bai wa Ukraine tallafin dala biliyan 4.5, kana ta ci gaba da taimaka mata na tsawon shekaru 10. Dama dai tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine, gwamnatin Kyiv ta sanya hannu a ire-iren wadannan yarjejeniyoyi guda 15 da kawayenta, irinsu su Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.
Karin bayani: Kungiyar G7 za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine
Zelensky ya kuma mika godiyarsa ga kasar Japan, da kuma jajjircewarta wajen mutunta dokar kasa da kasa. Ana sa ran Ukraine ta sake sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da Amirka kafin kammala taron da ke gudana a kasar Italiya.