1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin mamayar Isra'ila na shan suka

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 11, 2019

Kasashen Larabawa sun yi kakkauasar suka ga matakin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na mamaye wani kwari da ke yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.

https://p.dw.com/p/3PPoK
Israel, Jerusalem: Netanjahu hält Pressekonferenz zu Atompolitik Irans
Firaministan Isra'ila Benjamin NatanyahuHoto: Reuters/R. Zvulun

Firaministan Isra'ilan Benjamin Netanyahu dai ya ce zai mayar da kwarin karkashin ikon Isra'ilan in har aka sake zabarsa a zabe mai zuwa da za a gudanar a Isra'ilan a ranar 17 ga wannan wata na Satumba, zai kwace kwarin na Jordan wanda ke yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Tuni dai masarautar Saudiyya ta bayyana matakin da neman tayar da zaune tsaye, yayin da ministan harkokin kasashen ketare na kungiyar kasashen Larabawa, ya bayyana matakin da wani tarnaki ga kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Shima ministan harkokin kasashen waje na kasar Jordan Aiman ​​Safadi ya bayyana matakin da yin kafar ungulu ga kokarin wanzar da zaman lafiyar a yankin Gabas ta Tsakiyar.