Gabashin Ukraine na fuskantar mamaya
May 1, 2014Kwace iko da gine-ginen gwamnati na garin Donetsk da ke gabashin kasar ta Ukraine ke kara tabbatar da karfin 'yan awaren masu goyon bayan Rasha. Akwai wadanda suka samu raunika lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye, amma babu tabbacin dalilan yin haka.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha ya saka baki wajen ganin an sako masu saka ido na kungiyar tsaro da hadin kai a Turai da 'yan bindiga ke garkuwa da su. Tun ranar Jumma'a da ta gabata ake garkuwa da jami'an wadanda aka kama a wajen duba ababen hawa da ke garin Sloviansk.
Tuni wasu daga cikin mazauna yankin na gabashin Ukraine ke nuna damuwa da yadda masu dauke da makamai ke mamaye lamura, duk da yake kawo yanzu ba su fuskanci turjiya ba:
"Burinmu shi ne tabbatar da ganin kowa ya ajiye makami, babu wanda zai samu wani makami. Musamman idan 'yan yammacin Ukraine suka dauki makamai, ka fahimci abin da zai faru."
Waleri Heletej wani kwamanda na rundunar tsaron kasar ta Ukraine ya nunar da abin da ke faruwa na da alaka da zaben da ke tafe ranar 25 ga wannan wata na Mayu:
"Haka a fili yake saboda zaben shugaban kasa akwai zaman tankiya. Saboda hade yankin Kirimiya da Rasha, da halin da ake ciki a yankin gabshi, da kudu maso gabashi yankunan Donetsk da Luhansk zaman tankiya ya karu."
Ranar Laraba da ta wuce an tsare wasu jami'an sojin Rasha da ke aiki a ofishin jakadanci Ukraine na wani lokaci bisa zargin leken asiri, kafin daga bisani aka umurce su da ficewa daga cikin kasar. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya ce tattaunawa ce kawai za ta kawo karshen lamarin:
"Rasha ta yi imani tattaunawa tsakanin mahukuntan Kiev da masu adawa ya kamata, karkashin kungiyar tsaro da hadin kan Turai. Muna fata 'yan uwanmu na Yammacin za su kyale Ukraine ta fara wannan tattaunawa."
Sabbin mahukuntan wucin gadi na Ukraine sun shiga cikin wani yanayi na kasa hana abin da ke faruwa, kuma sun kasa tabbatar da doka da oda cikin kasar. Firamnistan kasar Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya ce zaben zai tabbatar da makomar kasar:
"Wannan zabe zai kunshi abin da ke damun kasar na hadin kai, iyakoki da kuma kara karfin ikon yankuna."
Hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF ta yi alkawarin bayar da kudaden da suka kai dala milyan dubu 17 wa kasar ta Ukraine domin daukan matakan farfado da tattalin arziki. Shugaban wucin gadi Oleksandr Turchynov ya amince da ayar dokar sojoji su tunkari mazuwar rikicin gabashin kasar.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal