1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabon: Dage lokacin zaben 'yan majalisar dokoki

Salissou Boukari
July 18, 2017

Kotun kolin kasar Gabon ta dauki matakin dage zaben 'yan majalisar dokokin kasar da ta kamata a yi a ranar 29 ga watan Yuli har ya zuwa watan Afrilu na 2018, bayan da a baya daman aka daga lokacin zaben.

https://p.dw.com/p/2gjZq
Gabon - Gerichtshof
Kotun tsarin mulkin kasar GabonHoto: Getty Images/AFP/S. Jordan

 Kudiri mai Lamba uku na hukuncin da kotun ta yanke wanda ta dauka a ranar 11 ga watan Yuli, ya ce zaben 'yan majalisar dokokin na Gabon za a shirya shi akalla cikin watan Afirilu na 2018. Dalillan daga zaben sun samo asali ne ta yanda aka kasa samun daidaito kan lokacin da hukumomin kula da harkokin zaben ya kamata su dauka na aiwatar da sauye-sauye kan tsarin zaben kaman yadda zaman taron sasantawa na 'yan siyasar kasar da shugaba Ali Bongo ya kira ya tsaida, zaman taron da madugun 'yan adawan kasar Jean Ping ya kauracewa. A watannin Afirilu da Mayu ne dai da suka gabata aka gudanar da zaman taron wanda ya bayar da shawarwarin kawo sauye-sauye kan harkokin zaben na Gabon.