1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabon: Roland Désiré Aba'a Minko ya shiga hannu

Salissou Boukari
June 28, 2017

Jami'an tsaro sun kame wani tsohon dan takarar neman shugabancin kasar Gabon mai suna Roland Désiré Aba'a Minko, wanda ya bai wa shugaban kasar Ali bongo wa'adin kwanaki uku da ya fice daga kan karagar mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/2fZ9U
Gabun Libreville Ausschreitungen nach Wahlen
Hoto: Reuters/Life Africa TV

Shi dai Aba'a Minko, ya ce muddin shuga Bongo bai sauka ba, zai tarwatsa duk wasu manyan ginenen ma'aikattun kasar kaman yadda babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Gabon Steeve Ndong Essame Ndong ya sanar da hakan a wannan Laraba. A ranar 16 ga wannan watan Yuni ne babban birnin kasar ta Gabon Libreville ya fuskanci rudanin da ake zarkin Aba'a Minko da haddasawa, bayan da mutanensa dauke da makammai irin su yukake da sanduna, suka kutsa kai a wasu gidajen kafofin yada labarai na gwamnati da masu zaman kan su, kuma suka isar da sakonni ga jama'a tare da neman saukar da gwamnatin Shugaba Bongo.

A halin yanzu dai ana ci gaba da gunadar da bincike a kan shi, inda ake zargin shi da laifuka da suka shafi tayar da zaune tsaye, da yada bayannai na karya dan haddasa rudu a cewar babban mai shigar da kara na gwamnatin ta Gabon, sannan kuma na nemen wasu da ake zargi da mara masa baya wajen wannan mataki na shi.