Gabon ta samu damar daukan nauyin gasar cin kofin Afirka
April 8, 2015An zabi kasar ta Gabon ta dauki nauyin gasar neman cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka a shekara ta 2017 nan da shekaru biyu masu zuwa. Hakan ya tabbata a zaben da aka yi tsakanin mambobin kwamitin gudanarwa 14 a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kasar ta Gabon ta samu nasarar a kan kasashen Ghana da Aljeriya wadanda suka nemi samun damar. Za a gudanar da wasan a filaye guda hudu da kasar take da su a Libreville, da Franceville, da Port Gentil da kuma Oyem. A shekara ta 2012 kasar ta Gabon da hadin gwiwan kasar Equatorial Guinea sun dauki nauyin gasar wanda kasar Zambiya ta lashe.
A wannan karo Gabon ta maye kasar Libiya wadda aka tsara za ta dauki nauyin gasar na Afirka a shekarar ta 2017, amma take ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula. Tuni aka fitar da jadawalin yadda kasashen za su kara wajen neman kai wa ga gasar neman cin kofin kwallon kafa na Afirka.