Gado mai tsatsa: Ra'ayin gurguzu a Afirka
Bukin nunin kayan tarihi na Gidan Iwalewa a Bayreuth mai taken "Lamura sun wargaje" daga farkon Tarayyar Sobiet zuwa wargajewar kasashen yammaci, ya mayar da hankali kan alakar Afirka da kasashe masu ra'ayin gurguzu.
Tsohuwar alaka: Sabuwar manufa
A yayin da kasashen Afirka suka samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a shekarun 1950, tuni masu mulkin mallakan suka fara yakin cacar baka. Inda suka fara fafutukar yada akidunsu a nahiyar ta Afirka, da take irinsu "Yakin Afirka-nasarar Afirka" inda ita ma Tarayyar Sobiet ta ci gajiyar sabbin kasashe.
Ragowar tsohuwar dangantaka
Alakar 'yan uwantaka tsakanin Tarayyar Sobiet da kasashen na Afirka dai bata je da nisa ba, amma ta bar tarihi har zuwa yanzu. A shekara ta 2006, mai daukar hoto na kasar Angola Kilonji Kia Henda ya ji alamun Karl Marx a wurin zubar da burbushin jiragen ruwa da ke arewacin Luanda. Jirgin daya daga cikin na kamun kifi da Tarayyar Sobiet ta bada gudummowarsa ga Angola.
Karamin yaki a nahiyar Afirka
Fitaccen mai daukar hoto na Afirka ta Kudu Jo Ractliffe, ya tunatar da tarihin alakar Angola da ra'ayin gurguzu ta hotunan wadannan shugabannin watau Leonid Brezhnev da Fidel Castro da kuma Agostinho Neto. A lokacin yakin basasan Angola, Cuba ta bada sojoji, ita kuwa Tarayyar Sobiet ta ba wa Netto makamai. A daya bangaren kuma akwai makamai da kudi daga Afirka ta Kudu da Amurka.
Yabon gwani ya zama dole: Kan sarki na Lumumba
Patrice Lumumba Firaministan Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na farko shi ma ya ya kasance mai bin ra'ayin gurguzu. Lokacin da kasarsa ta fada rikici ya nemi taimakon Tarayyar Sobiet. Daga bisani an yi masa kisan gilla, ta fille masa kai a bainar jami'an leken asirin kasar Beljium. Sanya hotonsa a kan sarki na nuna irin gudunmowarsa wajen fafutukar samar wa Afirka 'yanci.
Gayyata zuwa inda ba a maraba da kai
Mosko ta shigo da dalibai 'yan Afirka da ake nema. An sa su a jami'ar Patrice Lumumba da ke babban birnin kasar. Akasarinsu dai daukar nauyin karatun ne ke jan hankalinsu amma ba manufa ba. Sai dai kullum daliban na fuskantar kyama da wariya, batu da ya janyo bore. Zanga-zangar dalibai a shekarun 1950 ya zame boren farko a tarihi bayan na Stalin.
Leonid Brezhnev: Tasirinsa a nahiyar Afirka
Tarayyar Sobiet ta yi amfani da duk wata dama da take da ita wajen yada manufarta zuwa kasashen Afirka. An haramta daukar fim din ziyarar da Leonid Breschnev ya kai Guinea a shekarar 1957. Mai shirya fina-finai na tarihi Alexander Markov ya nunar da farfagandar da aka yi a wani fim da ya tsara, wanda aka zaba cikin fitattu a baje kolin fina-finai na 2015 a Berlin.
Hadin kai don ci gaba: Hotunan farfaganda
Aiwatar da farfaganda ta hanyar amfani da bayanai da hotuna ya kasance abu mai sauki, wanda ya samu karbuwa. Da hotunan yara uku daga nahiyoyi daban-daban, dole ne a samu nasara, wanda ke nuni da cewar, ba za a cimma wani ci gaba ba tare da hadin kai ba. Hakan ya kasance karfafa kwarin gwiwar yara da dama: Fatan shiga wannan balaguro tare don cimma manufa.
Bukukuwan taya 'yan gurguzu murna: Marx Engels a Addis
Ethiopia da ke zama matsugunin Kungiyar Tarayyar Afirka, na da muhimmanci ga nahiyar. Gwamnatin mulkin soji ta Mengistu Hailemariam, na da dalilai na gode wa Tarayyar Sobiet. Mutum-mutumin Marx wanda Erich Honecker ya kaddamar a bukin cika shekaru 10, shi ne abu na farko da duk wanda ya kai ziyara cibiyar Kungiyar ta Afirka zai yi ido hudu da shi. Yanzu haka hoton na a jami'ar Addis Ababa.
Gajiyar zamanin mulkin gurguzu: Mutum-mutumin Dakar
Har ya zuwa wannan lokaci, shugabannin Afirka na amfani da wani salo na gurguzu. Shugaba Abdoulaye Wade ne ya gina wannan mutum-mumin a shekara ta 2010 da lakabin suna "Sabuwar Afirka". Wani kamfanin Koriya ta Arewa ne ya gina, kamfanin da a baya yake samar wa Addis Ababa da sama da wasu kasashen Afirka 20, manyan kayayyaki.
Ainihin masu ra'ayin gurguzu
A shekara ta 2005 shugaban Botswana Festus Mogae ya kaddamar da wadannan gumakan guda uku, wadanda sarakunan gargajiya ne na kasar guda uku da ake kira "Dikgosi" da suka taka rawa a kasar ta yanzu. Fitaccen mai zane-zane na Koriya ta Arewa Onejoon Che, ke bayyana halayya na kaka-gida a kan mulki tsakanin shugabannin Afirka, wanda har yanzu ana samu.
Sauran abun da ya rage: Ouagadougou
Burkina Faso ta kasance kasa ta karshe da aka yi yunkurin kafa mulkin gurguzu. Ouagadougou ta kasance cibiyar fina-finai, saboda mutane kamar Ousmane Sembène da suka yi karatu a Mosko. Jami'in gurguzu Thomas Sankara ya taka rawa wajen daukar nauyin bukin nuna fina-finai na FESPACO.
Bude rassa a Afirka? Wargajewar Lamura
An gudanar da irin wannan nune-nunen kayan tarihin ne a London da Beyreuth. Bayan nan kuma za a gudanar da irinsa a birnin Budapest a watan Disamba. A yanzu haka dai gidan kayan tarihi na Iwalewa na tattaunawa da cibiyar nazarin al'adun gargajiyar Jamus na Goethe a kan yiwuwar bude rassansu a Afirka. Wannan shi ne fatan masu ra'ayin gurguzu.