Gambiya ta dakile yunkurin juyin mulki
December 21, 2022Talla
Gwamnatin Gambiyar ta bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu yayin da aka samu nasarar shawo kan al'amura a babban birnin kasar Banjul. Kawo yanzu dai babu wani tabbaci kan wadanda suka shirya wannan makarkashiyar.
A cikin sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce sojojin da aka kama a halin yanzu na taimakawa jami'an 'yan sanda da bincike yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum auku da ake zargin da kitsa juyin mulkin da bai samu nasara.
Ko a shekarar 2017, shugaba Barrow ya fuskanci yunkuri na juyin mulki, shekara guda bayan da ya dare madafun ikon kasar.