SiyasaAfirka
Fafutikar hukunta tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh
October 16, 2021Talla
Masu zanga-zangar a Banjul babban birnin kasar Gambiya sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta gaggauta cika alkawarin da ma'aikatar shari'a ta dauka na zartar da hukunci kan binciken cin zarafin bani Adama da wani kwamiti ya yi na tsawon shekaru biyu a yayin mulkin tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh.
Yahya Jammeh da yanzu haka ke gudun hijira sakamakon matsin lambar kungiyar ECOWAS, na da karfin fada a ji a cikin gida musamman ma a fagen siyasa. A baya-bayan nan ma an ambaci jam'iyyarsa da kulla kawance da ta Shugaba Adama Barrow da ke kan mulki, da niyyar tunkarar zaben shugaban kasa.