100509 Merkel Karsai Treffen
May 11, 2009Ƙasar na matuƙar buƙatar wannan tallafi don samar da zaman lafiya a cikinta. Ko da yake babu mai iya musanta wahalhalun da ake fuskanta amma Merkel ta yaba da cikakken haɗin kan da ake samu da hukumomin Afghanistan.
Jamus za ta ƙarfafa ayyukanta a Afghanistan. An jiyo haka ne daga bakin shugabar gwamnati Angela Merkel bayan ganawar da ta yi da shugaban Afghanistan Hamid Karzai a birnin Berlin. Ta ce za a faɗaɗa taimakon akan nasarorin da aka samu musamman a ɓangaren horas da ´yan sanda da sojojin Afghanistan.
"Ina ganin bai kamata a yi watsi da ci-gaban da aka samu a watanni da shekarun baya bayan nan ba. Dakarun tsaron Afghanistan na ɗaukar babban nauyi a birnin Kabul da kewayensa. Ko da yake a kullum rundunar ƙasa da ƙasa ta ISAF na mara musu baya amma shekaru biyu baya ba wanda ya yi zaton samun wannan ci-gaba."
To sai dai kashi 10 cikin 100 na dakarun tsaron Afghanistan ne suka samu horon da ya dace inji Merkel sannan sai ta ƙara da cewa.
"Har yanzu da sauran aiki a gabanmu wanda ya zama tilas mu gaggauta yin shi. Za a cike ƙa´idojin da suka wajaba domin fuskantar kyakyawar turbar da muka sa gaba. Dole sai mun zage dantse. A nan dai ba zan ƙarawa miya gishiri game da halin da ake ciki ba."
Merkel da Karzai sun goyi da bayan yin kwaskwarima ga dokar nan ta zaman aure da ake taƙaddama kanta wadda ta tilastawa matan aure musamman ´yan shi´a su riƙa biyawa mazan su buƙatunsu a kai a kai. Yanzu haka dai an gabatarwa majalisar dokoki shawarwarin yiwa dokar gyaran fuska, inji Karzai inda godewa Merkel game da taimakon da Jamus ke bawa Afghanistan.
"Ina miƙa gaisuwa da godiyar al´umar Afghanistan bisa taimakon da Jamus ta bawa Afghanistan a cikin shekaru bakwai da suka wuce, musamman a ɓangaren horas da ´yan sanda da sojoji da aikin sake gina Afghanistan da fannin kiwon lafiya da kuma ba da ilimi. Ina godiya ga kuɗi da sojojin da ku ka girke a ƙasarmu don ba da damar kyautata makomar al´umar Afghanistan."
Karzai ya jaddada cewa gwamnatin Afghanistan na samun sukunin tafiyar da aikinta a duk inda rundunar Jamus ta Bundeswehr ka jagorantar sojojin ISAF. Shugaban na Afghanistan ya yaba da aikin sojojin Jamus inda a makon da ya gabata suka kame wani ƙusa da ake zargi da ayyukan ta´addanci.
Merkel da Karzai sun nuna damuwa game da mawuyacin halin da ake ciki a Pakistan inda mayaƙan Taliban ke fafatawa da dakarun gwamnati, abin da haddasa kwararar dudun dubatan ´yan gudun hijira daga yankin kwarin Swat.
Mawallafa: Bettina Marx / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Hauwa Abubakar Ajeje