1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Angela Merkel da Sarki Abdullah na Jordan a Berlin

Zainab MohammedNovember 14, 2007

Rikicin yankin gabas ta tsakiya na cigaba da daukar hankalin Shugabanni

https://p.dw.com/p/CDrz
Merkel Da Sarki Abdullah na JordanHoto: AP

A yau ne Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Sarki Abdullah na II na Jordan suka gana a birnin Berlin,inda shugabannin biyu suka tattauna dangantakar kasashen su da kuma taron yankin gabas ta tsakiya da Amurka ke shirin ɗaukan nauyi a karshen wannan wata, a Annapolis dake jihar Maryland.

Wannan shine karo na uku da shugabar gwamnati Angela ta gana da Sarki Abdallah na Jordan cikin wannan shekara kadai,wanda mafi yawa daga cikin tattaunawar tasu bata shige halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya ba,musamman rikicin dake cigaba da gudana tsakanin kungiyar Hamas da Fatah,wanda ya haifar da karɓe madafan ikon zirin Gaza da Hamas tayi tun daga watan yunin daya gabata.

Adangane da taron na Amurka Sarki Abdullah na Jordan cewa ya yi.”muna fatan wannan taron kasa da kasa da zai gudana a Annapolis zai kasance wata kofa ce za ta buɗe na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin Izra’ela da Palasɗinu,da ma yankin baki ɗaya”

Tuni dai masu shiga tsakani da shugaba Mahmoud Abbas suka tattauna dangane da yadda yan ƙungiyar ta Fatah suka kaura cewa zirin Gaza zuwa gaɓar yamma da kogin Jordan.

Wa shugabar Gwamnatin Jamus Merkel ,ba bu dalilin wannan takaddama da saɓani tsakanin ɓangarorin biyu dake yankin Palasɗinawan,idan har ana muradin taron na Amurka yayi tasiri.

“Ina ganin samar da zaman lafiya a gaɓar yamma da kogin Jordan,zai taimaka matuka gaya wajen yin tasiri kan matsalolin tattali da zirin Gaza ke fuskanta.Kana samar da zaman lafiya a gaɓar yamma da kogin Jordan zai taimakawa shugaba Mahmoud Abbas da Premiya Fayyad wajen daidata dangantakar su da Izraela.Dangane da haka ne wannan ke zama wata dama na samar da cigaba”

Shugabannin biyu kaza lika sun kuma taɓo dangantakar kasuwanci tsakanin Jamus da Jordan,wanda suka ce dangantakar ba ta kai na siyasa ba.Sai dai Merkel ta tabbatar wa da Baƙon nata cewar ,dangantakar kasashen biyu ta fannin tattali da kasuwanci na da damar ingantuwa.

A yanzu haka dai Kamfanonin Jamus kalilan ne suke zuba jari a ƙasar ta Jordan,inji Sarki Abdallah.Kafin ya je birnin Berlin dai,Sarki Abdallah ya ziyarci Birnin Bremen dake nan tarayyar Jamus,inda ya halarci wani taro na dangantakar kasuwanci da kasashen ketare.

Sarki Abdullah yace mu na da sha’awar sabbin dabarun makamashi ,musamman ma makamashin iska,Jamus na ɗaya daga cikin ƙasashe da ke kan gaba ta wannan fannin,kuma wannan wata dama ce wa Jamus wajen inganta harkokin kasuwancin ta.Kaza lika muna da wasu ayyuka da suka haɗar da ayyukan samarda ruwan sha,da gina hanyoyin jiragen ƙasa,waɗanda a yanzu muke tuntuɓar jamus,mu na fatan shekarata 2008 za ta kasance na ingantuwan dangantaka tsakanin Jamus da Jordan.