Ganawar David Cameron da Angela Merkel a Berlin
May 21, 2010Talla
Sabon priministan Britaniya David Cameron ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a ziyararsa ta farko a birnin Berlin a matsayinsa na shugaban gwamnati. A taron manema labaru na haɗin gwiwa, Cameron da Merkel sun yarda da cewar daidaituwar kuɗin euro batu ne da dukkannnin ƙasashen Turai zasu yi maraba dashi, har da waɗanda basa amfani da euron. Sai dai shugabannin biyu sun samu saɓani akan tsaurin dokokin. Cameron yace ƙasarsa bazata amince da kowane sauyi akan yarjejeniyar EU da zai daɗa janyo Britaniya zuwa cikin yankin euro. Shugaban gwamnatin Britaniya ya bada goyon bayansa wa shirin Merkel akan kasuwannin hada-hada, wanda za a tattauna a taron ƙasashen G20 masu cigaban masana'antu.
Mawallafiya: zainab Mohammaed Edita: Umaru Aliyu