Ganawar farko tsakanin Trump da Al Sisi
April 3, 2017Talla
Shugaban kasar Masar Abdul Fattah Al-Sisi na ganawa da shugaban Amirka Donald Trump don sake kyautata dangantaka tsakanin kasashen da ta yi tsami cikin shekarun baya. Gabanin ziyarar ma dai an jiyo wasu sanatocin Amirka na cewa za su gabatar da batutuwan masu nasaba da goyon baya ga kasar Masar.
Shugaba Donald Trump dai bai boye kaunar da yake yiwa shugaba AL Sisi ba wanda ya kifar da gwamnati Mohammad Morsi a shekarar 2013. Shi dai shugaba Al Sisi mutum ne da ake zargi da take hakkin jama'a.
Ana kuma sa ran shugabannin biyu za su tattauna batun yaki da IS baya ga sabonta batutuwa na dangantaka tsakanin kasashen.