Ganawar Merkel da Rice
January 18, 2007Talla
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta ganada shugabar gwamnatin Jamus AngelaMerkel abirninBerlin,adangane da rangadin aikin data kammala a yankin gabas ta tsakiya.Wannan ganawar tasu dai tazo ne yini guda bayan Rice da takwaranta na nan Jamus Frank Walter-steinmeir sun sanar dacewa bangarori hudu dake tattauna warware rikicin yankin,zasu gudanar da taro a birnin washinton a farkon wata mai kamawa.Bangarorin hudu dai sun hadar da wakilan mdd da Amurka da Rasha da kungiyar tarayyar turai.Ana fatan cewa wannan ganawar tasu zata taimaka wajen bude sabon babin tattaunawa tsakanin izraela da palasdinu.Ayanzu haka dai Condoleeza Rice nakan hanyarta zuwa birnin London ,domin ganawa da prime minista Tony Blair.