1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Merkel da Sarkozy a kan rikicn kuɗi

August 16, 2011

shugaba Sarkozy na Faransa da Merkel ta Jamus za su tattauna game da rikicin kuɗi da ke addabar kasashen Turai. Sai dai batun fansar bashin da ya yi wa Girka da Italiya katuttu, ba ya cikin ajendar ganawarsu a Paris.

https://p.dw.com/p/12H3d
Angela merkel da Nicholas Sarkozy a taron manaima labaraiHoto: AP

Shugaba Nicholas Sarkozy na Faransa da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na shirin yi misayar yawu game da rikicin tattalin arzikin da ke addabar ƙasashe Girka da Italiya da ma dai wasu ƙasashe na duniya. shugabannin ƙasashen da ke da ƙarfin tattalin arzikin  za su kuma tattauna  game da barazanar da ƙasashen Amirka da kuma Faransa ke ciki na faɗawa cikin ruƙunin ƙasashe da za a rage bashin da ake basu.

 Wannan kuwa ya zo ne a daidai lokacin da  babban bankin Tarayyar Turai ya fanshi bashin wasu ƙasashen Eu da ya kai na kuɗi Euro miliyan dubu biyu, a matsayin wani mataki na ƙoƙarin shawo kan faɗuwar hannayen jari a kasuwannin hada-hada na duniya. Babban bankin dai ya fara aiwatar da wannan shirin ne a ƙoƙarin sa na sauƙaƙa matsin lambar da ƙasashen Girka da Portugal da kuma Ireland ke sha.

Masu gudanar da harkokin kasuwanci sun intifakin cewar bankin na turai yana mayar da hankali ne akan sayan shaidar hannun jarin ƙasashen Spain da kuma Italiya. Sai dai babban bankin na Turai, bai bayyana hannun jari ƙasashen da ya fansa ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman shehu Usman