1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Merkel da Sarkozy kan matsalar bashi

December 5, 2011

Yayin ganawar da suka yi a birnin Paris shugabannin Jamus da Faransa sun yi watsi da bukatar sayar da hannayen basukan da ake bin wasu kasashe masu amfani da kudin Euro

https://p.dw.com/p/13NCb
Nikolas Sarkozy da Angela MerkelHoto: dapd

An samu daideto tsakanin shugabar gwamatin Jamus Angela Merkel da shugaba Nikolas Sarkozy na Faransa kafin shiga taron da zai gudana a ranar 09-12-2011 domin gabatar da shawarwari game da matsalar bashi dake adabbar kasashe masu amfani da kudin Euro. To sai dai yayin ganawar da suka yi a birnin Paris shugabannin biyu sun bukaci yin sauye sauyen gaggawa a yarjejeniyar kungiyar Tarayyar Turai .To amma kasashe 17 da ke amfani da kudin euro ne kadai za su yi wadannan sauye sauye in har aka kasa cima matsaya tsakanin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai. Angela Merkel ta ce a watan Maris shekarar 2012 ne ake bukatar tantance wannan batu. Alal misali akwai bukatar shigar da doka kayyade bashi a kundin tsarin mulki na daidaikun kasashe masu amfani da kudin Euro. Merkel ta kuma mika bukatar kakaba takunkumi ba da wani kace na ce akan duk kasar da za ta take wannan doka . Merkel ta kuma yi kira da a gabatar da shirin ceto kudin Euro na dindindin kafin karshen shekarar 2011 a maimakon yin hakan a shekarar 2013. To sai dai Merkel da Sarkozy baki dayansu sun yi watsi da bukatar sayar da basuka ga banukuna.

A dai halin yanzu ana ci gaba da ka ce na ce game da bukatar yin sauye sauye a cikin yarjejeniyar Kungiyar Tarayyar Turai tsakanin kasashe mambobi abin da ake tsoron zai iya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe masu amfani da kudin euro da ke da alakar kut da kut da juna a bangaren guda da sauran kasashe mambobin kungiyar a dayan bangaren

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita; Yahouza Sadissou Madobi