1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar nasara a ganawar Trump da Kim

Alexander Freund Lateefa Mustapha Jaafar
June 13, 2018

A sharhin da ya rubuta Alexander Freund na DW ya ce tabbatar da aiwatar da abin da aka cimma a ganawar Shugaban Amirka Donald Trump da na Koriya ta Arewa Kim Jong Un na bukatar lokaci.

https://p.dw.com/p/2zU8x
Bildergalerie Kim Trump
Shugaban Amirka Donald Trump da na Koriya ta Arewa Kim Jung UnHoto: Reuters/J. Ernst

Alexander Freund ya fara sharhin nasa da ce wa ba a taba tsammanin Koriya ta Arewa za ta yi watsi da shirin makamin nukiliyarta domin samun tabbacin tsaro ba, kuma hakan yana da kyau matuka. A karshe, bayan watanni kalilan da aka yi tsammanin komai zai lalace baki daya lokacin da Shugaba Trump ya ayyana cewa ya fasa ganawa da shugaban Koriya ta Arewa kamar yadda aka tsara da kuma yadda shi ma a nasa bangaren Shugaba Kim ya yi gwajin makami mai linzami da ya fusata Majalisar Dinkin Duniya, a yanzu shugabannin biyu sun gaisa da juna tare da sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu. Trump ya yi kokarin gabatar da kansa a matsayin wani babban dan siyasa a duniya da ya kawo mafita a wani rikici da ake tunanin ba za a taba iya sulhunta shi ba. Duk da cewar Trump din a 'yan kwanakin nan ya yi wasu abubuwa da ake wa kallon basu kamata ba bisa hulda da kasashen ketare, kana duk da yadda ake masa kallon mutum mai gabunta, ya kasance shugaban da ya kawo karshen rashin jituwa ta tsawon shekaru tsakanin Amirka da Koriya ta Arewa, abin da tsofaffin shugabannin Amirka Clinton da Obama da suka kasance 'yan jam'iyyar Democrat da ma Bush babba da karami da suka kasance 'yan jam'iyyar Republicans basu yi ba, lallai ya kamata a jinjina wa wannan shugaba da ya kasance mazari ba a san gabansa ba.

Freund Alexander Kommentarbild App
Alexander Freund na DW

 A hannu guda kuma za a iya cewa Shugaba Kim Jong Un ma ya yi nasara, domin kuwa bayan da shugabannin biyu suka yi ta jifan juna da miyagun kalamai, sai ga shi daga bisani Shugaban na Koriya ta Arewa ya yi ganawar keke da keke da shugaban Amirka. Za a iya cewa karshen mulkinsa ba zai zamo tamkar na Saddam Hussein ko Gaddafi ba, ya yi kokarin kaucewa hakan. A lokaci guda kuma ya yi kokarin samun goyon bayan kasashen China da Rasha wadanda suka kasance a dakin taron na Singapor, haka ma kasar Japan wadda ba ta fatan ta rasa tasirin da take da shi a yankin ta hanyar kutsen Amirka. Da farko dai an dauki babban mataki na kama hanyar warware rikicin, sai dai kuma samun yadda da amincin zai dauki lokaci musamman a irin wadannan yarjejeniyyoyi da shaidan ba ya rasa kafar shiga ciki, kamar yadda Trump ya nuna dangane da yarjejeniyar nukilyar Iran. A yanzu da yankin Koriya ya samu kansa cikin irin wannan yarjejeniya, yadda Amirka ke shirin gabatar da kanta a yankin Asiya a nan gaba a bayyane ya ke: ta fuskacin tattalin arziki Amirka ba za ta iya ja da China ba sakamakon yanayin karfin tattalin arzikin China a yankin. A bangaren tsaro kuma Amirka har yanzu na ganin kanta a matsayin wadda ke da fada aji kana wadda za ta iya kawo gyara, ta yadda ta ke kokarin ganin ta tura China gefe guda. 

Ko a yayin ganawar ta kasar Singapor sai da Trump ya sake bayyana batun na Amirka ce ke iya gyara komai a duniya, inda ya ce idan jiragen yakin Amirka na shawagi a sararin samaniya ko kuma gabar ruwan abokan hulda, sako guda daya ne a ko yaushe: "muna mayar da martani ga abokan hamayyarmu China kana muna tare da kawayenmu." Ana dai kara samun kokonto kan ko Amirka za ta tura matasan sojoji zuwa filin daga, kamar yadda ta yi a shekaru 65 din da suka gabata yayin yakin na Koriya domin samar da 'yanci da demokaradiyya kila ma su mutu a can. A tsarinsa na "Amirka a farko" da karin haraji da watsi da yarjejeniyoyi, Trump ya rasa yarda a yankin Asiya. Za kuma a iya cewa taron mai dinbin tarihi na Singapor, ka iya kawo karshen tunanin da Amirka ke yi na cewa ita kadai ce za ta iya samar da tsaro ta kuma kawo gyara a duniya baki daya.