Hukumar yaki da cin hanci a Kano ta gayyaci Ganduje
July 6, 2023Talla
Hukumar ta KPCACC a jihar Kano ta bayyana cewar za ta bi duk matakan da doka ta tanada a kan tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje matukar ya bijirewa takardar sammacin da ta aika masa.
Hukumar na son tsohon gwamnan Kanon ya bayyana a gabanta dan kare kansa daga zargin karbar rashawa da ake yi mishi bayan ganin wani faifan bidiyo a shekarun baya.
Shugaban hukumar Barr Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewar suna sa ran tsohon gwamnan zai amsa gayyatar a makon gobe.
A shekarar 2017 ne aka fara sakin fefen bidiyon da ake zargin Ganduje ne yake karbar sunkin daloli yana cusawa a cikin aljihunsa, zargin da tsohon gwamnan ke musantawa ya na mai cewar fasahar zamani a kayi amfani da ita wajen kirkirar bidiyon.