Gandun dajin Hambach: 'Yan sanda na share sansanin 'yan fafutuka
Dajin Hambach da ke zama mafi girman wurin hakar ma'adinan kwal a Turai, ya kasance wata alama ta tirjiya daga masu fafutukar kare muhalli. A ranar 13.9.2018 kamfanin wuta na RWE ya fara aikin share gandun dajin.
Lokacin da lamari ya tsananta
Bayan tsawon lokaci, a ranar Alhamis (13.09.18) 'yan sanda suka fara rusa gidajen da masu boren suka yi a kan bishiyoyi a dajin Hambach. Da yawa daga cikin masu fafutukar kare muhallin da suka jima a dajin ba su nuna tirjiya ga yunkurin 'yan sandan ba. A hukumance, rusa gidajen na da kariya daga dokar kaucewa barkewar gobara.
Rayuwa a cikin gidajen kan bishiya
Tsawon shekaru shida kenan, matasa tsakanin 100 zuwa 200 ke rayuwa cikin gidajen, wanda ke zama dan yankin da ya rage da dajin na Hambach. An samar da karamin kauye da gidaje a kan bishiyoyi. Masu fafutukar na amfani da boren ne wajen kare ci gaban share dajin. An gabatarwa kotun gudanarwa da ke birnin Kwalan takardun koken rusa gidajen kan bishiyoyin.
Neman taimako daga mai sama
Gabanin daukar matakin rusa gidajen dai, an gudanar da addu'o'i na musamman a cikin dajin. A fafutukarsu ta tabbatar da adalci ga muhalli har ya zuwa taron muhalli na Majalisar Dinkin Duniya na COP24 a Katowice, Rev Martje Mechels ta gudanar da addu'o'i ga mazauna dajin. Sai dai addu'o'i sun gaza hana rusa wadannan matsugunai.
Kamfanin hakar kwal da kare muhalli
Dalilin da ya janyo boren adawar kenan a wannan daji. Kamfanin makamashi na RWE na shirin share yanki na karshe na dajin Hambach. Tuni dai aka lalata kashi 90 na dajin da aka hake don aikin kwal. A watan Oktoba ne kotun gudanarwa ta garin Münster za ta zartar da hukuncin karshe kan halalcin hakar ma'adinan, tsakanin kamfanin makamashi na RWE da masu fafutukar kare muhalli.
Rokon dakatar da rusa gidajen
Watan Augusta 2018: Mafi karancin shekaru daga cikin 'yan fafutukar bai cika shekara daya ba. Yunkurin kamfanin RWE na rusa kauyen ya harzuka masu adawa da hakar ma'adinan. Masu kare muhalli da kauyuka da ke makwabtaka da 'yan siyasa na kira da a dakatar da RWE daga ci gaba da share filin, har zuwa karshen shekara. Lokacin da kwamitin gwamnati kan kawo karshen hakar kwal zai gabatar da rahotonsa.
Masu yawon bude ido a dajin duk ranar Lahadi
A ranar Lahadi masanin gandun daji Michael Zobel kan yi bayani ga masu ziyara kan dajin Hambach. A bangaren tsohon dajin, akwai wasu nau'o'i na tsuntsaye da shekarunsu ya kai 300. Kazalika akwai wasu tsuntaye da ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa, da ke samun mafaka a dajin Hambach. Duk wadannan bayanai ne da masu yawon bude idon ba su sani ba.
'Yan fafutukar na da hadari?
A 'yan makonni da suka gabata dai, jami'an 'yan sanda sun ruwaito cewar masu boren na jifansu da duwatsu da makamantansu. Amma mafi yawa daga cikin mazauna dajin, mutanen kirki ne, kamar wadannan matasan biyu masu fafutuka da ke rike da na'urar kashe gobara. Sai dai 'yan sanda kan bayyana irin wannan a matsayin na'ura mai hadari da kan iya fashewa.
Rashin sahihin doka
A watan Augusta ne kwararre kan hakar kwal Dirk Jansen ya fadawa kwamitin kwal din halin da ake ciki. Sai dai kamfanin makamshi na RWE ya yi wa kotun gudanarwa ta Münster alkawarin jiran sakamakonta, kan halalcin hakar ma'adina na kwal. Tuni dai wata karamar kotu ta halalta aikin. Sai kamfanin na RWE ya ce ba zai iya jira fiye da ranar 14 ga watan Oktoba ba.