Gangamin adawa da kyamar Yahudawa a Berlin
September 14, 2014Shugaban babbar majalisar Yahudawa Dieter Graumann ya yi kira ga Jamusawa da su kara bajimta wajen yaki da masu kyamar Yahudawa. A wani taron gangami da majalisar ta shirya dandalin kofar nan ta Brandenburg da ke Berlin, Graumann ya ce yakin Gaza da aka yi a lokacin bazara ya ta da wani yanayi na kyamar Yahudawa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta kasance babbar bakuwa mai jawabi a gangamin da ya hada mutane kimanin 6000, ta yi kira da a nuna turjiya ga masu kyamar Yahudawa, inda ta kara da cewa.
"Da sunan gwamnatin Jamus ina Allah wadai da kowane irin nau'i na kyamar Yahudawa a Jamus da ma Turai baki daya. Ina mai watsi da dukkan kalaman batanci da aka yi wa Yahudawa albarkacin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu na baya bayan nan, inda aka yi amfani da wannan damar wajen nuna kyama ga Yahudawa saboda manufofin gwamnain Isra'ila."