Gangunan sinadarin uranimum sun bace a Libiya
March 16, 2023Talla
Daractan hukumar Rafael Grossi ya ce kimanin ganguna 10 ne na sinadarin uranium din ne masu bincike suka gano, sai dai a yanzu sun yi batan dabo a wani wurin da ba a bayyana ko ina bane.
Grossi ya ce, babban abun damune dauke sinadarin kuma hakan ka iya haifar da matsalolin tsaro na nukiliya. Hukumar IAEA dai ta ce za ta gudanar da bincike domin gano hakikanin dalilin kawar da sinadarin da kuma wurin da aka kai shi saboda gudun fadawa hannun bata gari. A shekarar 2003 ne dai tsohon shugaban kasar Libiya, Moammar Gadhafi ya amince da yin watsi da shirin kera makaman nukiliya, wanda a karkashin shirin ya amincewa masu binciken makamai shiga kasar.