1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankado kabari a Sudan

Suleiman Babayo MAB
July 13, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bankado kabari da aka binne mutane da dama da ake zargin rundunar mayar da martani da aikata wannan ta'asa.

https://p.dw.com/p/4TqzP
Mata a yankin Darfur na Sudan
Yankin Darfur na SudanHoto: Abd Raouf/AP/picture alliance

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an bankado wani kabari da aka binne kimanin mutane 87 a yankin yammacin Darfur na Sudan. Hukumar ta ce tana da sahihan bayanan cewa rundunar mayar da martani ta aikata kisan.

Volker Turk shugaban hukumar ta kare hakkin dan Adam ta Majaliyar Dinkin Duniya ya tabbatar da haka cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Alhamis.

Haka na zuwa lokacin da kasar Masar ta ce ta amince shiga tsakanin sojojin kasar ta Sudan da ke fafata yaki da mayakan rundunatr mayar da martani. Kimanin watanni uku da suka gabata yaki ya barke tsakanin sojoji da rundunar mayar da martani lamarin da ya kai ga mutuwar kusan mutane 3,000 yayin da wasu kimanin milyan uku suka tsere daga giudajensu.