SiyasaJamus
Gargadi ga Isra'ila bisa mamayar yankin Falasdinu
July 7, 2020Talla
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Jamus ta fitar, ta ce gamayyar kasashen gami da manyan abokan Isra'ila biyu da ke yankin Gabas ta Tsakiya sun ce tuni ministocin harkokin wajensu suka fara tattaunawa tsakanin ita Isra'ila da kuma Falasdinu.
Tun a shekarun 1967 ne Yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mamaye yankin na Falasdinu. A baya bayan nan dai shugaban Amirka Donald Trump ya bai wa Isra'ila damar mallakar yankuna da dama na Gabar Yammacin kogin Jordan, wanda Falasdinawa suka ki amincewa da hakan.