1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadin Taliban ga masu zabe a Pakistan

May 10, 2013

'Yan kungiyar Taliban a Pakistan sun gargadi masu kada kuri'a a kasar da su kauracewa zaben da za a gudanar a kasar a gobe domin tsira da rayukansu.

https://p.dw.com/p/18VPZ
--- 2013_04_09_Themenbild_wahl_pakistan.psd
Themenbild Wahl Pakistan 2013 Urdu

Mai magana da yawun kungiyar a kasar ta Pakisatan Ehsanullah Ehsan ne ya yi wannan gargadin a wannan Juma'ar inda ya ce kungiyarsu ta shirya kai hare-hare rumfunan zabe domin hana gudanar zabe don a cewarsa hakan ya sabawa ka'idojin shari'ar musulunci.

To sai dai duk da wannan barazana ta kungiyar ta Taliban, hukumar zaben kasar ta ce za a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara hasalima ta samar da takardun kada kuri'a isassu gami da akwatunan zabe yayin da jamian tsaro su ka ce su na cikin shirin ko ta kwana domin ganin an gudanar da zaben ba tare da wata tarzoma ba.

Takara dai a zaben na gobe za ta fi zafi ne tsakanin Nawaz Sharif da ke son darewa kan kujerar firaministan kasar a karo na uku da kuma shahararren dan wasan kurket din Imran Khan wanda ake ganin zai taka rawar gani a zaben.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe