Gasar Olympic ta bazara mafi nasara
Samun zinare na Olympics mafarki ne ga 'yan wasa da yawa. Wasu na sarrafa shi fiye da sau guda amma ga wannan rukunin fitattun, ya zama al'ada. A nan ga jerin masu tara lambobin yabo mafi daraja a gasar ta bazara.
Usain Bolt - Zinare sau 8
Ko dai zinare ko ba komai - da alama wannan shi ne taken 'yan tsalle-tsallen kasar Jamaica. Usain Bolt ya lashe lambobin yabo na Olympics guda takwas a rayuwarsa, kuma dukkan su sun kasance zinare. Ya lashe tseren mita 100 da na mita 200 a birnin Beijing a shekarar 2012 da kuma zinare a tseren mita 4x100 wanda ya hada a birnin Landan 2012 da kuma a Rio de Janeiro na Brazil a 2016.
Ray Ewry - Zinare sau 8
Kamar Usain Bolt, Ray Ewry shi ma yana da tarihin gasar Olympics. Amma tarihin ya nuna cewa bai kai ga matsayi na biyu ba. Duk da faman da ya yi da cutar shan inna tun yana yaro da ya kai ana tura shi a keken guragu a wasu lokuta, Ba’Amurken ya lashe gasar guje-guje da tsalle-tsalle sau uku a jere a tsakanin shekarar 1900 zuwa 1908.
Matt Biondi - Zinare sau 8 Azurfa 2 da kuma Tagulla sau 1
Dan wasan ninkayan Amurka ya lashe lambobin zinare biyar daga cikin takwas na zinare a gasar wasannin 1988 a birnin Seoul. Ya lashe tseren mita 50 da 100 kafin ya ci gaba da samun nasara sau uku tare da tawagar Amurka. Hakan ya biyo bayan nasarar da aka samu a shekarar 1984 kafin ya kara wasu zinaren guda biyu a 1992 a Barcelona na kasar Spain.
Jenny Thompson - Zinare sau 8, Azurfa sau 3 da kuma Tagulla 1
Jenny Thompson matashiya ce mai ban mamaki: Ta lashe zinare na Olympics sau takwas tsakanin 1992 zuwa 2000, wanda ya sa ta zama 'yar wasa mafi nasara a tarihin gasar Olympics. Ko da yake ba ta taɓa yin nasara a matsayin 'yar wasa ita kadai ba, sai dai a matsayin bangaren kungiyar zari-ruga. Ta lashe azurfa a tseren mita 100 a shekara ta 1992 da kuma tagulla a 2000.
Sawao Kato - Zinare sau 8, Azurfa sau 3 da kuma Tagulla 1
Fitaccen dan wasan motsa jikin kasar Japan yana daya daga cikin 'yan wasa 4 kacal da suka sami nasarar wasannin Olympics a dukkanin fannoni. Sawao Kato ya shiga gasa sau uku ta Olympics a 1968 zuwa 1976 kuma ya lashe lambobin yabo 12, takwas daga cikin su zinariya. Bayan lokacinsa na dan wasan motsa jiki, ya koyar a matsayin farfesa a fannin kimiyyar lafiya da wasanni a Jami'ar Tsukuba.
Birgit Fischer - Zinare sau 8 da Azurfa sau 4
'Yar wasan da ta fi samun nasara a Jamus, ita ce 'yar wasan kwale-kwale da ta samu lambar yabo ta zinare takwas a Olympics da kuma azurfa hudu ga Jamus ta Gabas, sannan kuma a hadaddiyar Jamus. Birgit Fischer ta halarci gasar Olympics shida a cikin shekaru 24 masu ban mamaki, tsakanin 1980 da 2004. Ita ce mafi girma da kankantar shekaru da ta lashe zinare a tseren kwale-kwale.
Carl Lewis - Zinare sau 9 da Azurfa 1
Ba'Amurke Carl Lewis ya mamaye wasan tsallen badake da gudu a shekarun 1980 da 1990. A cikin shekarar 1999, Hukumar Kula da Wasanni ta Duniya (IAAF) ta karrama shi a matsayin dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na karni. Sai dai a 2003, ya yarda cewa ya sha haramtattun abubuwa kafin ya cancanci shiga gasar Olympics ta 1988, amma kuma kasar Amurka ta wanke shi.
Mark Spitz - Zinare Sau 9 Azurfa 1 da Tagulla 1
Spitz zai kusan shiga wannan jerin ne saboda gasar Olympics ta 1972 kadai, inda ya lashe lambar zinare bakwai a Munich. Shekaru hudu da suka gabata a birnin Mexico, ya lashe lambobin zinare biyu a fannin gudu, da azurfa da tagulla. Daga nan sai ya yi ritaya ba zato ba tsammani; yana da shekaru 22 bayan gasar Munich kafin ya yi yunkurin dawowa a makare, yana da shekaru 41, a 1992.
Paavo Nurmi - Zinare sau 9 da azurfa sau 3
Dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Finland ya lashe lambobin yabo na Olympics guda goma sha biyu tsakanin 1920 zuwa 1928 kuma ya tsaya saman filin wasa sau tara. Paavo Nurmi ya kafa tarihin duniya 24 a wurare daban-daban. A shekarar 1931, ya tallata maganin Rejuven, wanda yanzu aka haramta. Bayan shekara guda, an dakatar da shi har tsawon rayuwarsa saboda keta matsayinsa.
Larysa Latynina - Zinare sau 9 Azurfa 5 da kuma Tagulla 4
A zahiri, Larysa Latynina ta yi mafarkin zama ’yar wasan ballet, amma lokacin da mai ba ta horo ya kaura, sai ta koma wasan motsa jiki tana 'yar shekara 11. Nan take ta zama 'yar wasa mafi nasara a sabon wasanta. Ta tsaya a kan dandamali a gasar Olympics sau 18, kuma a samansa sau tara a tsakanin shekarar 1956 da 1964. Bayan ta yi ritaya, ta yi aiki a matsayin mai horar da tawagar Tarayyar Soviet.
Michael Phelps - Zinare sau 23 Azurfa 3 da Tagulla 2
Dan wasa ke nan na Olympia mafi nasara a kowane lokaci a kusan kowane ma'auni. Michael Phelps shi ne ke da lambobin zinare 23, da lambobin hadin gwiwa masu yawa. A wasanni 8, wadanda 6 duk suka kasance zinare, da ya samu a Beijing a 2008. Har ya ce zai yi ritaya bayan gasar Landan a 2012, amma ya dawo ya kare da karin zinare biyar da lambar azurfa daya a Rio a shekarar 2016.