1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni ya tabo gasar Sashen Afirka na DW

Suleiman Babayo
September 10, 2018

A cikin shirin Labarin Wasanni na wannan lokaci, akwai sakamakon wasan kwallon kafa na sashen Afirka na DW da ya wakana a karshen mako, akwai kuma batun kakar wasannin Bundesliga na Jamus da ke gudana a yanzu.

https://p.dw.com/p/34ci6
Deutschland Bonn - DW Afrika Cup 2017
Shugaban sashen Afirka na bayar da kofiHoto: DW/W. Mwaura

A wannan mako ake komawa kakar wasan lig na Bundesliga na Jamus, inda a ranar Jamma'a za a fafata tsakanin Borussia Dortmund da Eintracht Frankfurt, kafin a kece raini a ranar Asabar tsakanin Wolfsburg da Hertha Berlin, ita kuma Düsseldorf da Hoffenheim, anata Bangaren Leipzig za ta kara da Hannover. Yayin da Mainz za ta karbi bakuncin Augsburg.

Fußball 1. Bundesliga | Borussia Dortmund v RB Leipzig (3:1)
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Kirchner

A wannan makon mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Jamus Joachim Loew, ya fara matakin musamman na farfadowa, bayan rashin nasara ta ba zata a lokacin wasan cin kofin kwallon kafa na duniya da ya gabata a kasar Rasha. A wasannin sada zumuncin da suka gabata na karshen mako, Jamus ta samu nasara kan Peru da ci 2 da 1, kana ta tashi babu wanda ya jafa kwallo a raga tsakaninta da Faransa wacce ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

A wasan Tennis na karshe da aka kara a karshen mako Naomi Osaka daga kasar Jampan ta samu nasarar lashe babbar gasa ta farko, bayan ta doke daya daga cikin gwanayen wasan Serena Williams 'yar Amirka. Hukumar kula wasan Tennis ta Amirka ta ci tarar Serena Williams bisa wasu kalaman da ake zargin ta yi, sai dai a cewar Williams wannan nuna banbanci ne ga mata domin 'yan wasa maza sun fadi kalaman da suka fi nata daci kuma babu abin da ya faru.

Deutschland Bonn - DW Afrika Cup 2017
Hoto: DW/W. Mwaura

Idan muka dawo nan Tashar DW a karshen mako aka kare gasar Sashen Afirka tsakanin sassan Afirka na DW, kuma a bana Sashen Turancin Ingilishi ya samu nasarar lashe gasar a gaban sashen Faransanci. Sai dai kuma Sashen Hausa ya taka rawa ta ba yabo ba fallasa.