1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gawarwaki a rikicin Shi'a da 'yan sanda a Kano

November 14, 2016

Rikici dai ya barke tsakanin mabiyan na shi'a karkashin kunigiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wadanda ke tattaki tsakanin jihar Kano zuwa jihar Kaduna.

https://p.dw.com/p/2Sgj8
Nigeria Schiitische Muslime in Dakasoye
'Yan Shia dai kan yi tattaki daga sassa daban-daban na Najeriya zuwa jihar ta KadunaHoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

A kalla mutane 10 ne suka rasu yayin da wasu da dama suka sami raunuka bayan wata taho mu gama da aka yi tsakanin 'yan Shi'a a wajen birnin Kano Arewa maso Yammacin Najeriya kamar yadda wasu da suka sheda lamarin da ma 'yan sanda.

Rikici dai ya  barke tsakanin mabiyan na Shi'a karkashin kunigiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wadanda ke tattaki tsakanin jihar Kano zuwa jihar Kaduna dan bikin ranar Ashura.

Ilyasu Ammani wani da ya sheda lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya ga mutane 15 kwance a kasa kafin daga bisani 'yan sanda su kwashe su. Ammani dai ya ce ya ga wannan adadi a inda fadan ya kaure a kwanar Dawaki a wajen birnin na Kano. A cewar majiyar 'yan sanda dai sun yi harbi ne bayan da wani daga cikinsu ya fiskanci barazanar rayuwa a hannun 'yan kungiyar ta Shi'a karkashin IMN.