SiyasaIsra'ila
Shirin tsagaita wuta na watanni biyu a Gaza
January 23, 2024Talla
An mika tayin ga masu shiga tsakani daga Masar da Qatar, in ji tashar labarai ta Axios Abin da zai ba da damar sako dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su, da har yanzu Hamas ke rike da su a zirin Gaza. Sannan a labarin da jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka ta fitar, ta ce kasashen Larabawa ma suna aiki kan shawarar samar da kasashe biyu bayan kawo karshen yakin. A saboda haka, Saudiyya ta yi tayin amincewa da Isra'ila a matsayin mayar da martani ga kafa kasar Falasdinu.