1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJojiya

Georgia: Za a sake kidayar kuri'u a wasu mazabu

Abdullahi Tanko Bala
October 29, 2024

Hukumar zabe a kasar Georgia na shirin sake kidaya kuri'un wasu mazabu bayan da yan adawa suka yi korafin cewa an tafka magudi na satar kuri'iu. Sai dai shugaban kasar ya yi kiran gudanar da bincike na kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/4mNJq
Zanga zangar adawa da sakamakon zabe a Georgia
Zanga zangar adawa da sakamakon zabe a GeorgiaHoto: Irakli Gedenidze/REUTERS

Alkaluman sakamakon da hukumar zaben ta fitar a farko ya nuna jam'iyya mai mulki ta Georgian Dream Party na kan hanyar lashe zaben da gagarumin rinjaye inda ta sami kusan kashi 54 cikin dari na kuri'iun da aka kada.

Sakamakon ya kuma nuna kawancen Jam'iyyu hudu na adawa sun sami kashi 38 cikin dari na kuri'un

Jam'iyyun adawar dai da kuma shugabar kasar Salome Zourabichvili wadda ta yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin Firaminista Irakil Kobakhidez sun ce an tafka magudi.

Dubban jama'a sun fita titunan Tbilisi don nuna fushinsu da sakamakon zaben.