1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gerhard Schröder ya yi ban kwana da fagen siyasa.

YAHAYA AHMEDOctober 13, 2005

Tun da jam'iyyun siyasa na CDU da SPD suka yarje kan kafa gwamnatin hadin gwiwa ne, ake ta rade-radi kan makoma da kuma irin mukamin da Gerahrd Schröder, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus na yanzu, zai rike. To yanzu dai, shugaban mai barin gado, ya fito fili ya bayyana cewa, ba zai shiga cikin wata sabuwar gwamnati ba. Ya yi ban kwana da fagen siyasa, gaban dimbin yawan magoya bayansa a wani jawabin da ya yi musu a birnin Hannover.

https://p.dw.com/p/BvYp
Gerhard Schröder, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus mai barin gado.
Gerhard Schröder, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus mai barin gado.Hoto: AP

A birnin Hannover, inda yake da zama ne, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus mai barin gado, Gerhard Schröder, ya ba da sanarwar cewa, ba zai shiga sabuwar gwamnatin da za a kafa karkashin jagorancin Angela Merkel ba. Ya dai ba da wannan sanarwar ne gaban kungiyoyin kwadago na masana’antun hako ma’adinai, da na sarrafa makamashi da kuma sinadari. Su dai wadannan kungiyoyin, sun ne suk nuna wa Schjrödern cikakken goyoyn baya, a lokacin da ake ta zanga-zangar nuna adawa ga matakan da gwamnatinsa ta gabatar na farfado da tattalin arzikin Jamus.

Bisa dukkan alamu dai, Gerhard Schröder, ya zabi wannan lokacin ne, kusa da gidansa, kuma tsakanin magoya bayansa, kafin ya ba da sanarwar, wadda tun da ma can ake ta rade-radi a kanta. A cikin `yan makwannin da suka wuce dai, an yi ta zaton cewa, watakila shugaban zai rike wani mukami a sabuwar gwamnatin. Saboda shi da kansa ma, ya sha nanata wa maneman labarai cewa, jam’iyyarsa ta SPD ce za ta yanke shawara game da yadda ababa za su wakana.

Da can dai, musamman a ranar da aka gudanad da zaben, Gerhard Schröder, ya bayyana cewa, gwamnatinsa ce kawai za ta iya ceto Jamus daga komadar tattalin arzikin da take huskanta. Kuma shi ne zai ci gaba da jagorancin wannan gwamnatin. Sai dai, jam’iyyarsa ba ta sami kuri’un da take bukata don ya iya cim ma wannan burin ba.

A lokacin yakin neman zabe, shugaba Schröder ya nuna matukar kwazo wajen shawo kan dimbin yawan magoya bayan jam’iyyar ta SPD, wadanda suka nuna alamun hasala da manufofin da gwamnatin ke bi, su jefa masa kuri’a. Ta hakan ne dai jam’iyyar ta sami kuri’u fiye da yadda aka zata, duk da cewa dai, ba su kai yadda za ta sami cikakken rinjayi na kafa gwamnati ba.

A halin yanzu kuma, a karshen wa’adinsa, shugaba Schröder na samun cikakken goyon bayan jam’iyyar. A cikin jawabinsa na ban kwana, shugaban mai barin gado ya fada wa al’umman birnin Hannover cewa, ya na sha’awar dawowa gida, inda yake da asalinsa, bayan janyewarsa gaba daya, daga fagen siyasa.

Amma har ila yau dai, wasu masharhanta na ganin cewa, wannan ban kwanar da Schröder ya yi da fagen siyasa, ba ta karshe ba ke nan. Zai iya dawowa ba zato ba tsammani a dandalin siyasar, inda kuma zai iya kasancewa daya daga cikin wadanda sai an dama da su. Ba abin mamaki ba ne kuma a sake ganin shi rike da wani muhimmin mukami.