Ghana: Jam'iyar adawa ta yi ikirarin lashe zabe
December 9, 2016Shugaban babbar jam'iyyar adawa a Ghana Nana Akufo-Addo , ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a wannan Larabar.
Ya ce "Da sakamakon da aka samu kawo yanzu, mun lashe karin 49 daga cikin yawan kujerun majalisa. Kuma muna da yakinin cewar zaben shugaban kasa ma mun lashe. Sai dai zamu yi dakon sanarwar hukumar zabe"
Ghana dai na zama kyakkyawar misalin demokaradiyya a nahiyar Afirka, wadda zabenta ke gudana kusan cikin lumana. Karo biyu tun daga shekarata 2000, al'ummar kasar ke kayar da shugaban da ke kan kujerar mulki.
Akwai tafiyar hawainiya a kidayar kuri'un da aka kada, sai dai sakamakon da ke fitowa daga kasar na nuni da cewar, jam'iyyar adawa ta NPP ce ke gaba kana NDC ta shugaba mai ci John Mahama Dramani ke biye da ita.