1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana na fama da karancin kujeru a makarantun firamare

Inshola Yussif Abdul Ganiyu MAB
December 27, 2023

Kimanin dalibai miliyan 2.3 a makarantun firamare da sakandare (JHS) na kasar Ghana na fama da karancin tebura da kujerun zama a aji, lamarin da rahoton da Eduwatch ta fitar ke cewa babbar barazana ce ga harkar ilimi.

https://p.dw.com/p/4acS8
Makarantun karkara na fama da karancin kujeru a arewacin Ghana
Makarantun karkara na fama da karancin kujeru a arewacin GhanaHoto: Fotolia/Living Legend

Rashin kayan karatu na ci gaba da yin kamari a Ghana, lamarin da ya sanya cibiyar da ke kula da harkar ilimi mai suna African Education Watch ta ce ana bukatar kujera da teburan zaman dalibai guda miliyan 1.5 a cikin gaggawa. Rahoton ya kara da cewar gwamnatin Ghana na bukatar 330 miliyan ma kudin kasar don magance gibin kayayyin koyarwa musamman ma kujeru da ake fama da shi.

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu na taimakawa wajen samar da kujeru ga dalibai a Accra
Wasu kungiyoyi masu zaman kansu na taimakawa wajen samar da kujeru ga dalibai a AccraHoto: Imago/F. Stark

Malami Bashiru Muhammad da ke karantarwa a arewacin Ghana ya ce wasu daga cikin dalibai na zama ne a kan tabarma, alhali kujeru na da muhimmanci wajen neman ilimi domin suna hana litattafai da tufafin dalibai yin dauda.Amma masana harkar ilimi suka ce matsalar karancin kujerun zama ta fi kamari a yankin karkara na kasar Ghana.

Malam Suleiman Alhassan Faransi da ke yaki da jahilci ya ce Ghana za ta yi da-na-sani idan ba ta mayar da hankali a kan ilimin manyan gobe ba. Shi kuwa dalibi Umar Ali ya ce zama a kasa a cikin aji na hana shi mayar da hankali kan darasi.