Nasarar sulhunta rikici a wajen kotunan Ghana
August 30, 2022A kasar ta Ghana dai, akwai alkalai sama da 420 da ke fama da dubban shari'u masu daukar lokaci ba tare da an warware su ba. Hakan ta sanya kasar bullo da tsarin sasantawa, inda akasin yadda kotuna kan dauki lokaci suna bin bahasin shari'un, su wadannan kotuna na tafi da gidanka na da dabarun shirya wadanda suka fusata da juna. Sama da shekaru 10 ke nan da samar da wannan tsari na Alternative Dispute Resolution ADR, a takaice. Tsari ne kuma da masu ruwa da tsaki a harkokin shari'a ma suka ce, ya kawo sauki ga kotunan Ghana da ke fama da shari'u a cewar Abassitimi Awenatey, jagorar shirin na shiga tsakani a yankin arewacin kasar.
Ya zuwa yanzu dai akwai kamanin rigingimu dubu 29 da aka yi kiyasin masu shiga tsakanin sun iya warwarewa tun bayan fara aikin samar da sulhun, abin da kotunan kasar ma ke farin ciki da shi. Alkalin alkalai a Ghanan, Justice Anim Yeboah ya nuna bukatar sanya tsarin sosai cikin harkokin shari'a a baki dayan kundin dokar gudanar da hukunci ta kasa. Yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu bukatar tsarin sulhu na shiga tsakani a Ghana, har yanzu akwai wasu da dama da suka fi son kotu ta yanke musu da hukunci kan korafe-korafen da suke da su.