Motoci kirar Ghana na samun karbuwa a kasar
October 28, 2015Kasar Ghana kamar sauran takwarorinta na Afrika na dogaro ne da albarkatun kasa da da take da su wajen samar da kudaden shiga da kuma gudanar da ayyuka. Shekaru da dama albarkatun man fetur da zinare da kuma ganyen koko, sun kasance kan gaba wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Sai dai Ghana na amfani da makudan kudade a kasashen ketare domin sayo kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa. Misali ana shigo da kayan gyaran motoci masu tsada daga kasashen ketare. To amma wani dan kasuwa na son kawo sauyi a kasar kuma ba wai zai fara da kadan-kadan bane, yana son ya kafa babbar masana'antar kera motoci ne a Ghanan. Da zarar ka kalli motocin sun yi kama da motocin sintiri da ake amfani da su a Afirka, sai dai ba haka bane. Motar samfurin Pickup ta banbanta da sauran. Kirar Kantanka ce da aka kera a Ghana. Cephar Arthur shi ne jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandar kasar ta Ghanaya kuma tabbatar da ingancin motocin yana mai cewa:
"In kana da mota kamar wannan, za ta baka damar yin sintiri da bai wa al'umma tabbacin tsaro, kana zaka tsoratar da masu laifi. Ta na da matukar amfani."
Akasarin bangarorin motocin ana shigo da su ne daga kasar China, sai dai wasu a gida ake kera su. Akwai ma'aikata kimanin 300, da ke hada motocin ta hanyar yin amfani da injinan da za su iya aiki ko a lokutan da aka samu daukewar hasken wutar lantarki. Dukkan aikin suna yin shi ne da hannu babu mutum-mutumi wato Robot da ke taimaka musu. Kwadwo Safo Senior ne ya samar da masana'antar a yanzu kuma dansa Kwadwo Safo Junior ke tafiyar da ita a matsayin shugabanta. Kuma ya yi tsokaci kan fatan da mahaifin nasa ke da shi yana mai cewa:
Kyakkyawan fata da cikar buri
"Ya yi imanin cewa duk abin da aka sarrafa a kasashen yamma za a iya yi a gida. Ya yi imanin cewa ba saye ne kawai aikinmu ba, ya yi imanin cewa muma za mu iya kirkirar fasaha."
Kwadwo Safo Senior ya yi fice sosai a Ghana. Yana da kamfanoni masu yawa ana kuma kiransa da mai bushara wato “Apostle“ kana yana da Coci kuma shi ne shugaban Cocin nasa. Tun kafin ya fara kera mota ya yi abubuwa da dama wadanda ake ganin ba masu yiwuwa bane, ya fara da yin kayayyaki tun daga ganguna masu amfani da hasken wutar lantarki har ya zuwa Talabijin da ake sarrarfawa ta hanyar yin tafi. Da zarar mutum ya tafa hannunsa sai ya sauya tasha.
Motoci kirar Kantanka
Sun samu nasarar kera mota da ke gargadin masu wucewa da su kauce a cikin harshen Twi na Ghana a yayin da take komawa da baya. Tana kuma amfani da wutar lantarki. Al'ummar kasar ta Ghana dai na da fata a kan kamfanin hada motocin.
Ya ce: "Farashin ya zamo mai sauki domin mu masu karamin karfi mu iya saya." Wannan kuma cewa ta yi: "Muna da duk wadannan motocin masu tsada, amma idan muna da wadanda aka hada a Ghana, in farashin na da sauki kuma akwai inganci kamar na kasashen wajen mai zai hana mu saya." Shiko wannan cewa ya ke: "Ya na taimakawa wajen bunkasa kasa da samar da ayyukan yi ga matasa."
Kawo yanzu dai suna hada motocin ne idan wani ya bukata kuma kadan kawai suke yi. Sai dai nan gaba kadan Kwadwo Safo Junior na son ya hada kai da masu sari na cikin gida wajen sayar da motocin. Farashin motocin samfurin Pickups da SUVs ya kama Euro 15.000 da kuma Euro 22.000, kusan farashi guda da wanda aka shigo dasu daga kasashen Asiya. Kamfanin ya ce zai yi wasu samfurin masu arha, kana yana fadada ayyukansa.