SiyasaAfirka
Ghana ta haramta yi wa mutane zargin maita
October 24, 2023Talla
Matakin ya biyo bayan kisan wata tsohuwa mai shekaru 90 a garin Kafaba da ke yankin Gonja a gabashin jihar Savana a arewacin Ghana, wacce aka jefe har lahira.
Kungiyoyi masu rajin kare hakkokin bil Adama sun koka a kan jinkirin da shugaban kasar ke yi wajen rattaba hannu kudirin domin zama doka.
Camfe-camfe na tsafi ko zargin tsafi da maita ba sabon abu bane a Ghana. Wadanda a kan zarga da kuma iyalansu kan shiga mawuyacin hali sakamkon wariya ko tswangwama da a kan yi musu.