1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata masu juna biyu da masu shayarwa na cikin damuwa a Ghana

Maxwell Suuk ZMA/MNA
December 17, 2019

Kashi 13 daga cikin 100 na mata masu juna biyu ko masu jego bayan haihuwa na fuskantar matsalar tawaya bayan haihuwa, saboda bakin ciki da yawan damuwa da kuma tsananin nakuda da sukan tsinci kansu a ciki.

https://p.dw.com/p/3UxLY
Symbolbild- Mutter stillt Baby
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Kokoroko

A kasashe masu tasowa matsala ta tawaya bayan haihuwa ta fi kamari saboda yanayi na zamantakewar al'umma da halin ko oho ta mazaje ga matansu da ke dauke da juna biyu, wanda a wasu lokuta ya kan kai har ga rasa ran mai jegon ko kuma jaririn da ta haifa.

Tun bayan da wata kungiya mai zaman kanta ta majami'ar Roman Katolika ta kaddamar da wani shiri na taimaka wa mata masu juna biyu da masu jego da jariransu, aka samu koma bayan yawan samun damuwa a tsakanin matan.

Wannan kungiya kan gudanar da zama na mahawara ta mata masu juna biyu da ke yankunan karkakara, suna fadakar da su hanyoyin da za su bi don faranta wa rayuwarsu, kuma hakan na taimaka wa rayuwar matan.

Munaya Alhassan mai shekaru 39 da haihuwa, sannu a hankali tana farfadowa daga tawayar bayan haihuwa, da aka danganta da halayyar mijinta, ta bayyana halin da take ciki.

"Bayan na sha wahala wajen haihuwar 'ya'ya bakwai da wannan mutumin, an wayi gari rana daya ya ce ba zai iya ci gaba da daukar nauyinmu ba. Ya ce in ci gaba da kula da kaina da 'ya'yana. 'Yar autata makonninta shida kacal. Na yi ta rokonsa amma ya ki. Daga bisani na roki filin da zan rika yin noma. Ban samu wani amfanin kirki ba. Hakan ya jefani cikin damuwa har na so kashe kaina, saboda mene ne amfanin rayuwar? Duk saboda abin da mijina ya yi min."

Ghana Mutter mit Baby
Hoto: picture-alliance/dpa/Nana Kofi Acquah/MamaYe Ghana

Yanayin da wannan mata ta tsinci kanta a ciki ba wani abu sabo ba ne, saboda mata da dama a kasar Ghana na cikin irin wannan hali na shiga damuwa kafin da kuma bayan haihuwa sakamakon dalilai da dama da suka hadar da nakuda mai tsawo da talauci da rashin kulawar maza. Kamar yadda wannan matar ke cewa.

"A kullum ina cikin sumbatu ni kadai saboda yawan tunani. Mutane na ganin na samu tabin hankali, saboda abin da namiji ya jefani ciki."

Gungun matan da suka yi hakuri da irin muzgunawar da mazajensu ke musu kan yi wata zama a gindin wata bishiyar mangwaro, suna jajantawa juna, inda kowacce ke ba da nata labarin, da neman mafita don kaucewa fadawa cikin yanayi na damuwa. Kowacce ta fuskanci matsaloli masu nasaba da fargaba ko kuma damuwa.

Alkaluma na nuni da cewar a fadin duniya musamman a Afirka kaso 13 cikin 100 na kasancewa cikin matsanciyar damuwa kafin da bayan haihuwa a kowace shekara. Denisia Lugtuah ungozoma ce, wadda ta ce abin mamaki ne irin matan da ke samunta cikin hali na damuwa.

"Wasu magidantan ba su da karfin kulawa da matansu. Don haka idan suna cikin nakuda ko bayan haihuwa, sukan fada cikin matsalar rashin abinci, saboda samun ruwan nonon da za su bai wa jaririnsu. Magidanta da dama ba sa iya kulawa da iyalansu, wanda hakan ke jefa matan cikin damuwa, saboda tunani. Ina yawaita samun irin wadannan koke-koken."

Idan har ana neman sauyi, wajibi ne a shawo kan matsalar talauci da zuba jari a harkokin kiwon lafiya na karkara. Amma a arewacin Ghana wannan shiri da ya fara da matakin kula da jarirai na samun nasara.