Ghana: Zabe ya gudana lafiya
December 1, 2016Talla
Al'ummar kasar Ghana sun gudanar da zaben shugaban kasa ranar bakwai ga watan Disambar nan na shekarar 2016 ba tare da fuskantar wani kalubale babba ba. Takara dai ta fi zafi ne tsakanin shugaban kasar mai ci yanzu John Dramani Mahama da kuma Nana Akufo-Addo sai kuma wasu 'yan takara abiyar da suka hadar da dan takarar Independa.