1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Ghana sun yi zanga zanga

Abdullahi Tanko Bala
August 4, 2021

Dubban matasa sun yi tattaki a Accra babban birnin kasar Ghana a wani matakin adawa da gwamnatin shugaba Nana Akufo-Addo a zanga zangar da suka yi wa take a "gyara kasa".

https://p.dw.com/p/3yY7F
Ghana | Fixthecountry Proteste in Accra
Hoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Sanye da jar taguwa da bakaken wanduna suna rera wakokin kishin kasa, masu zanga zangar sun rika daga kwalaye da aka yiwa rubutu da ke cewa "Cin hanci na haifar da talauci" wasu kuma na cewa "A gyara tsarin Ilmin mu a yanzu"

Matasan sun karade tituna a babban birnin kasar. Zanga zangar ta yau Laraba ita ce ta baya bayan nan tun watan Maris a jerin zanga zangar adawa da gwamnati bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da yan adawa suka shigar na kalubalantar nasarar sake zabar Akufo-Addo a bara.

Nana Akufo-Addo ya sami nasarar tazarce karo na biyu a karagar mulki da kankanin rinjayen yan majalisar dokoki. Sai dai tun daga wannan lokaci shugaban ke fuskantar matsin lamba yayin da kasar ta yammacin Afirka ta fada matsalolin tattalin arziki wanda ya kara tabarbarewa sakamakon annobar corona.